Gwamnatin tarayya ta gargadi mutane da su daina cin naman ganda
A tsaya da cin ganda yanzu, gwamnatin tarayya ta gargaɗi ƴan ƙasa bayan ɓullar sabuwar cuta
Gwamnatin tarayya ta sanar da ƴan ƙasa game da barkewar cutar Anthrax a wasu kasashe makwabta na yankin yammacin Afirka.
Dr Ernest Umakhihe, babban sakatare na ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a yau Litinin.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito Ya ce kasashen da abin ya shafa su ne, Arewacin Ghana mai iyaka da Burkina Faso da Togo.
Mista Umakhihe ya ce cutar da ta yi sanadin mutuwar wasu mutane, cuta ce ta kwayoyin cuta da ke shafar dabbobi da mutane.
Ya ce a dabi’ance ana samun kututturen Anthrax a cikin kasa kuma yana shafar dabbobin gida da na daji.
Mista Umakhihe ya ce mutane na iya kamuwa da cutar ta Anthrax idan suka hadu da dabbobi masu dauke da cutar ko kuma gurbatattun kayayyakin dabbobi.
Ya ce cutar ba mai yaduwa ba ce, inda mutum ba zai iya kamuwa da ita ta hanyar kusantar mai dauke da cutar.
“Alamomin anthrax sune, alamun mura, kamar tari, zazzabi da ciwon tsoka,” in ji shi.
Saboda haka ya ke shawartar ƴan ƙasa da su dakata da xin banda a halin yanzu har zuwa a shawo kan lamarin.