Labarai

Bidiyon Wasu Masoya Suna Shakatawa a Ɗakin Otel Ya Girgiza Intanet

Wata matashiyar ‘yar Najeriya kuma kyakkyawar budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan wani bidiyo da ta ɗauki kanta da wani ɗan saurayi da take kira da, “Papi na.”

Jaridar Legithausa na ruwaito A wani shafin dandalin TikTok @thatgirlese18, budurwan ta wallafa bidiyon wanda ya nuna ita da masoyinta sun kwanta kan gado a wani wuri da ake kyautata zaton ɗakin Otal ne.

Yayin da ɗan bawan Allah ya yi nisa a bacci harda wangame baki, ita budurwan kam idonta biyu kuma ta yi amfani da wannan damar wajen ɗaukar bidiyonsu tare.

Ta waiga ta kalle shi ta gani ko ya farka daga bacci amma ta ga mutumi na ta sharar barci abinsa, daga nan ta ci gaba da ɗaukar bidiyonta tana ƙara gyarawa

Ga bidiyon nan

@thatgirlese18♬ original sound – Bionation

Bidiyon ya ja hankalin masu amfani da kafar TikTok kuma mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu musamman ganin matashin bai da wasu shekaru da yawa.

Martanin wasu mutane kan bidiyon budurwar da matashin saurayin

Fawaz ya ce: “Ya haka ne kar ki rufe masa baki, ki bar ɗan bawan Allah ya huta mana.”

Ola Para ta ce:

“Haba dai wannan ba saurayinki bane, ai ƙaramin yaro ne, inda ya cika matashi kuma saurayi ba zai yi kalar wannam barcin ba.”

Glory Bilz ta rubuta cewa:

“Zamani ya kawo mu mata basu barin mutun ya cika shekara 18 kafin su fara kiransa da Papi na.”

Vawulence ya maida martani da cewa:

“A duk abinda zaka yi a rayuwa kar ka kuskura mace ta riƙa rigaka farkawa daga bacci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button