Kannywood

Yan damfara Sun sace Motar Jaruma Fati Muhammad bayan Sun Yaudareta

Fitacciyar Jarumar Kannywood Fati Muhammad ta bayyanawa Dala FM yadda wasu ƴan damfara suka sace mata Mota bayan sun nemi samar mata maganin magauta.Yan damfara Sun sace Motar Jaruma Fati Muhammad bayan Sun Yaudareta

Jarumar ta bayyanawa Gidan radiyon Dala FM cewa wani dan uwanta me suna sulaiman Kyawa yazo har gida ya sameta inda yake fada mata cewa yar uwa gaskiya kina cikin wani Hali amma zan hadaki da wani abokina malamine sosai kuma zai taimakeki domin Magauta suna jifarki da yawa kuma dole dama ba Za’a barki a haka ba.

Jarumar taci gaba da cewa Sulaiman ya kira abokinsa me suna malam isah wanda ya fada mata cewa malamine Sannan ya fada Masa cewa dan Allah ga wata yar uwarsa nan ga kuma abinda yake damunta don haka yana so ataimaka mata.

Malam isah ya aikowa Jarumar da rubutu hade da wasu magunguna Wanda zata sha da kuma hayaki da zata ringayi, a Cewar ta bayan tayi amfani dasu Kamar yadda malam isah ya umurceta daga nan sai Hankalin ta ya gushe Washe gari shi kuma Sulaiman Kyawa ya gudu da motar ta.

Yan Sanda sunyi Nasarar Kama Malam Isah inda ya bayyana masu cewa shifa sunan shi Muhammad Sani ba malam isah ba kuma shiba malami bane.

A karshe dai jarumar ta bayyana cewa Yan sanda suna nan sunaci gaba da Neman Sulaiman, ta kuma shawarci sauran yan uwanta Yan Fim dama Al’umma baki daya cewa su guji yadda da mutane lokaci daya domin a karshe ba lalle abun yayi kyau ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button