Labarai

Ya kamata a ƙirƙirar wa tsoffin matan shugabannin ƙasa wani gata bayan sun bar mulki — Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa mai barin gado, Aisha Buhari, ta yi kira da a yi amfani da wasu gata irin na samar da ababen hawa, daukar nauyin tafiye-tafiye na neman lafiya da bayar da wasu alawus-alawus da ake baiwa tsoffin shugabannin kasar, ga matan shugabannin kasa.Ya kamata a ƙirƙirar wa tsoffin matan shugabannin ƙasa wani gata bayan sun bar mulki — Aisha Buhari

Daily Nigerian Hausa na ruwaito Buhari ta ce matan shugaban kasa sun cancanci wannan gata kamar yadda mazajensu ko Shugabanni suke a ofis da kuma barin ofis rashin aiki saboda idan matsin lamba ya zo, ba wanda yake son sanin ceww ko kun fita daga Villa ko a’a.

Aisha Buhari ta yi magana ne a wajen kaddamar da wani littafi a Abuja wanda shugabar kungiyar matan jami’an tsaro da ‘yan sanda (DEPOWA), Misis Vickie Anwuli Irabor ta rubuta mai suna, “Rayuwar matar Soja”.

Da ta ke bayyana dalilin da ya sa za a kara wa matan shugabannin kasa wannan gata, Misis Buhari ta ce, “Na auri mijina a matsayin matar tsohon shugaban kasa. Zan tafi nan da ‘yan kwanaki a matsayin matar tsohon shugaban kasa karo na biyu.

“Ya kamata su dauke mu a matsayin matan tsohon shugaban kasa. Kamata ya yi su hada da matan shugaban kasa, su ba mu wasu gata da muka cancanta a matsayinmu na matan shugaban kasa, ba wai tsoffin shugabannin kasa kadai ba”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button