Ta Auri Maza Biyu Suna Kwana Ɗaki Ɗaya Tare
Wata mata ta samu kanta cikin auren mazaje biyu, inda dukkan su suke rayuwa a gida ɗaya, ɗaki ɗaya kuma suke cin abinci tare. Haka kuma har sun haifi ’ya’ya daban-daban.
Matar mai suna Francine Jisele, ‘yar ƙasar Congo, ta shaida wa jaridar Murango News cewa tana son mazajen nata biyu sosai, duk kuwa da cewa tana samun ƙunci da rashin sukuni a duk lokacin da za ta yi kwanciyar aure da ɗayansu.
“Da son samu ne, ya kamata a ce muna zaune a gidaje daban-daban, sai dai hakan ba ta samu ba. Don haka a duk lokacin da zan yi saduwar aure da ɗaya, dole ɗayan ya fita daga ɗakin. Amma duk da haka ina son su duka kuma muna rayuwa cikin jituwa da junanmu.” In ji Francine.
Da take bayanin yadda aka yi ta auri mazaje biyu, matar ta shaida wa jaridar cewa a baya mijinta na farko mai suna Remi Murula, sun yi aure ne shekara 7 da ta gabata, wanda suke da ‘ya’ya biyu. Ta ce matsalar rayuwa ce ta sanya ya gudu, ya bar ta da ɗawainiyar neman abinci.
“A faɗi-tashin neman abinci ne na haɗu da mijina na biyu, mai suna Albert Jarlace, muka yi aure, bayan na shaida masa yadda mijina ya gudu ya bar ni da yara biyu,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa, suna zaune da mijin nata na biyu, har ta haifi yaro ɗaya sai ga mijin na farko ya dawo. Don haka ita kuma ta ce tana son su duka, don haka suka daidaita, suka ci gaba da aure – mace ɗaya miji biyu.
A nasa ɓangaren, mijin nata na farko, Remi ya yi nadamar guduwa tun da farko. Ya ce laifinsa ne ya haddasa faruwar wannan al’amari.
SHARHI:
Darasin da ke labarin nan yana nuni da kyan tsari da ingancin Musulunci, wanda ya haramta irin wannan aure.
Rahoto Daga
Taskar_Gizago