Hausa Series Fim
Sanarwa akan Fim Din LABARINA Season 7 – Daga Aminu Saira
Fitaccen mai bada umurni darakta Malam Aminu saira wanda shine mai bada umurni a cikin wannan kayatacen shiri mai dogon zango shirin labarina wanda anka kammala zango na shidda a turance ‘season 6’.
Labarina shiri ne wanda ya samu mabiya sosai a cikin wannan shiri inda miliyoyon mutane suke kallo wanda ya samu karbuwa kasa Nigeria da nahiyar Afirka baki daya.
Malam Aminu saira ya fito da muhimmiyar sanarwa akan sabon shirin labarina ta yadda za’a dawo da ci gaba da haske wannan shiri mai dogon zango domin an tafi hutu kafin watan Ramadan.
Darakta yana mai cewa
” Muna nan muna aiki ba dare ba rana in sha Allahu nan gaba kadan zamu sanar da ranar da za’a dawo .”
Ga dai sanarwa nan a cikin faifan bidiyo sai ku saurara.