Kannywood

Daga Karshe Adam A zango ya fitar da matar aure da ranar aure 

Fitaccen mawaki kuma jarumi adam a zango bayan ya fitar da matar aure bayan ya rabu da mai dakinsa safiya chakalawa.

Adam a zango ya shiga rudani inda yake tunanin kila zai auri Alul- kitabi wato Kiristan ko bayahudiya inda kowa yake ta mamaki irin wannan kalamai sosai.

Akwai wani rubutu da yayi inda yake cewa a shafinsa na sada zumunta.

Na hadu da wata yar china jiya mun fara maganar aure ya kuke gani.

Ku bani shawara?.

Daga Karshe Adam A zango ya fitar da matar aure da ranar aure 

Bayan anyi cece kuce akan wannan furuci nan take kuma sai ga jarumin ya fitar da hoton wata mata tare da Date din aure cikin raha.

SAVE THE DATE 17/03/2023 YANZU MUNAFUKAI ZASUCE BATAYI!”

Daga Karshe Adam A zango ya fitar da matar aure da ranar aure 

Amma mutane suna mamakin miyasa ya sanya wannan date bayan watan ya wuce amma wasu kuma suna ganin cewa raha ce kawai.

Hausaloaded ta tattaro martanin mutane akan wannan furuci.

@ Nuradeen Argungu: Wannan baki kadaibi a hankali kada takaima cixo

@Abubakar sunoma Mustapha: Kaida ka zabi abin ka wallahi tayi,
Allah ya tabbatar Allah yasa daga ita ka rufe karin aure, ALla yasa ta zama ta gari che, Allah ya baku ikon bawa juna haqqi

@Auwal sani : Dan Allah Adamu kadaina irin wadanan magaganu nibana jindadi sabida ni masoyinkane nahaqiqa duk lokachinda akafadamaka baqar magana raina yana matuqar 6achi wlh Duk da bakasanniba nabarka lafiya.

@abdumudallab222 : Kai da Kai ran tsawa da Allah bazaka sake aure ba

Adam a zango ya mayar masa martani cewa : @abdumudallab222 TOH YANZU NA FASA MATA 2 BIYU ZANYI LOKACI GUDA..

@habeeybu : wanda yaci kai ya huta

Adam a zango ya mayar da martani cewa : @habeeybu ai chin kai duniya ne

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button