Mustapha Nabraska Yayiwa Rarara Martani mai zafi kan sabuwa wakarsa
Na Rantse Da Allah Rarara Ka Gama Zagin Kwankwaso Domin A Wannan Karon Sai Mun Dauki Mataki, Inji Nabraska
Fitaccen jarumin nan Mustapha Badamasi wanda akabfi sani da Nabraska ya fito fili ya nuna damuwarsa akan sabuwar waƙar da mawaƙi Rarara ya saki, inda Nabraska ya bayyana cewa “na kasa gane abinda ya sake jan hankalin Rarara har ya sake zagin Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, mene ne kuma ya ba shi sha’awa wajen zagin iyayenmu, shugabanninmu, sannan wanne mutum Rarara yake so ya burge idan ya zagi Kwankwaso?
Nabraska ya ƙara da cewa ya kasa gane burin da mawaƙin yake so ya cika idan ya zagi Kwankwaso.
“Duk wanda kake so ka burge idan ka ba shi dama ya zagi Kwankwaso kowanene ba zai zage shi ba, Kwankwaso baya ta kai, harkar neman abinci ai ba hauka bane,”.
Nabraska ya yi rantsuwa da Allah cewa “tabbas Rarara ya gama zagin Kwankwaso domin a wannan karon akwai mataki na doka da kuma Shari’a da za su ɗauka. Don haka komai mawaƙin ya gani a ƙwaryar cin tuwonsa.
Ga bidiyon nan kasa ku saurara daga bakin jarumin.