An Koresu Daga Aiki : Yan sanda masu baiwa Rarara kariya
Yanzu nan majiyarmu ta samu wannan labari daga shahararin marubucin nan Datti Assalafiy ya ruwaita wannna labari a shafinsa na sada zumunta.
Rundinar ‘yan sandan Nigeria ta kori wasu jami’an ‘yan sanda guda uku wadanda suke bawa mawaki Dauda Kahutu Rarara kariya daga aiki
Rundinar ta koresu daga aiki a yau alhamis bayan ta kama jami’an nata da laifin harba bindiga sama haka siddan a lokacin da suke tare da mawaki Rarara don su burgeshi a kauyensa na Kahutu dake jihar Katsina ranar 7-4-2023
Jami’an ‘yan sandan sune:
(1) Inspector Dahiru Shuaibu
(2) Sgt Abdullahi Badamasi
(3) Sgt Isa Danladi
Suna aiki da rundinarsa ‘yan sanda masu bada kariya na musamman Special Protection Unit (SPU) rundina ta daya dake Kano
Kunga abinda na fada shekaran jiya bayan an kamasu an kaisu Abuja, nace Rarara ya ja musu, gashi yau an koresu daga aiki, don haka Rarara sai ya biyasu diyya
Wallahi na tausaya musu, kuma na tausaya wa iyalansh, wannan lokacin ba lokaci bane da kana jami’i zakayi abinda zaka burge wani ko wasu, karshe zaka jefa kanka a matsala
Allah Ya basu mafita na alheri