Kannywood

An kama yan sanda masu baiwa Dauda Kahutu Rarara kariya

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa an kama wasu ‘yan sanda da ke ba shahararren mawakin nan na Kano Dauda Kahutu Rarara kariya.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga ‘yan sandan da ke ba mawakin kariya suna bin sa a baya har ya shiga mota bayan haka suka soma harba bindiga a sama.An kama yan sanda masu baiwa Dauda Kahutu Rarara kariya

Kamar yadda majiyarmu ta samu wannan labari daga gidan jaridar Trt Afrika Hausa Sai dai a wani sako da mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya Muyiwa Adejobi ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce rundunar ‘yan sandan kasar ta yi tir da “rashin kwarewa da kuma halaye na rashin ɗa’a da ‘yan sandan suka nuna inda suke harba bindiga domin kuranta mawakin na Kano.

“An gano ‘yan sandan kuma an kama su. Za a kai su hedikwatar ‘yan sanda domin yi musu tambayoyi da kuma daukar matakan da suka dace,” kamar yadda ya kara da cewa.

Haka kuma ya ce irin wannan ɗabi’a ba ta ‘yan sanda ba ce kuma ba za su lamunci hakan ba.

Ɓata-gari

Sai dai a wani bidiyon wata hira da aka yi da mawakin, ya musanta cewa ‘yan sandan sun yi harbi domin nishadi inda ya ce wasu ne suka yi niyyar tayar da tarzoma suka yi harbin.

“Mun je muna rabon abinci a Kahutu, sai wasu bata-gari suka shigo suna neman su tayar da tarzoma, a nan wurin ne muka samu matsala ‘yan sandanmu suka yi harbi sama,” in ji Rarara.

Ya bayyana cewa dalilin da ya sa ‘yan sandan ba su harba hayaki mai sa hawaye ba saboda ana azumi.

A kwanakin baya ne dai wasu matasa suka far wa gidan mawakin a Jihar Kano inda suka kona wani sashe na gidan tare da kwashe wasu kayayyaki.

Sai dai daga baya ‘yan sanda sun samu nasarar gano wasu matasan da kuma kwato kayayyakin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button