Labarai

Kisan Ummita: Ba da niyyar kisa na daɓa mata wuƙa ba, in ji ɗan China da ya hallaka budurwarsa a Kano

Wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47, a yau Alhamis ya tabbatarw wata babbar kotu a Kano cewa ya daɓa wa budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita wuka.

Wanda ake tuhumar, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, na ci gaba da gurfana ne a gaban kotun bisa laifin kisan kai.

Kisan Ummita: Ba da niyyar kisa na daɓa mata wuƙa ba, in ji ɗan China da ya hallaka budurwarsa a Kano

Daily Nigerian Hausa na ruwaito Frank da lauyan masu gabatar da kara ke yi masa tambayoyi, Darakta mai shigar da kara na jihar Kano, DPP, Aisha Mahmoud, ya shaida wa kotun cewa a wannan ranar da ibtila’in ya afku, abubuwa da dama sun faru.

Ya shaida wa kotun cewa ya zo Najeriya ne a 2019 domin yin aiki a matsayin Manajan Kasuwanci da Tallace-tallace a Kamfanin BBY Textile Kano.

“Ana biya na Naira miliyan 1.5 duk wata kuma ina yin wasu harkokin daban-daban. A ranar da kaddarar ta afku, Ummukulsum ta tura ni kan gado.

“Na caka mata wuka ne ba tare da niyyar kashe ta ba.

“Na fita daga dakin ta taga tunda an kulle kofa daga waje ina so in kai Ummukulsum ɗin asibiti amma sai ‘yan sanda suka iso suka kama ni,” in ji Mista Frank.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button