Kannywood

Kalli yadda hadiza Gabon ta wulakanta wani wahalalle da yayi mata wakoki har guda 7

Ɗazu na kalli Bidiyon wata jarumar wasan kwaikwayo da wani matashi yayi mata waƙa har guda 7.

A cikin bayanin ta tace ita baya son ayi mata waƙa kuma ko anyi bata saurare. Ba wannan ya sanya ni yin magana.

Abun da ya fi ɗaukar hankali shine inda jarumar take cewa “Idan ka yiwa mutum waƙa ka na expecting wani abu a hannun sa ne”Kalli yadda hadiza Gabon ta wulakanta wani wahalalle da yayi mata wakoki har guda 7


Ya kamata matasa mu daina cusa kai da ƙwaɗayin abun hannun mutane.

Wani abu da na yarda da shi a rayuwa shine, idan har ka ƙware a wani abu (skills) da zaka iya amfanar mutane da shi, ba ka da buƙatar tumasanci a wajen kowa a duniya kuma ko mutum baya sonka dole ya nema ka idan kana da rana a wajen sa.

Kusan 90% na mutanen da suke da wani abu a rayuwa ko sannu ka yi musu tunani suke wani wabu kake roƙo a Wajen su.

Matasa dan Allah a natsu a rage cusa kai, duk duniya babu wanda zai maka abun da Allah bai maka. Da zarar ka ƙware a skills sannan ka koyi mu’amala, ka da kayi kokwanto akan cewa arzikin ka na hanya daga Allah da yake bayarwa.

A sha ruwa lafiya.

Saurara ga bidiyon nan ka kalla.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button