Kannywood

Hotuna: Furodusa Abdul Amart Mai kwashewa yayi Murna Shekara 7 da Aurensa

Fitaccen furodusa Abdul Amart mai kwashewa yayi murna bikin shekara bakwai 7 da aurensa wanda Allah ya baiwa yaya tare da wannan mata inda yayi take mata ta a duniya mata ta a aljannah innsha Allah kamar yadda ya wallafa kalmaai na godiya ga mahalicinsa Allah. Ga rubutun kamar hakaHotuna: Furodusa Abdul Amart Mai kwashewa yayi Murna Shekara 7 da Aurensa

Mata ta a duniya kuma Mata ta a Aljannah in sha Allah

Yau shekara 7 daidai da Allah ya Azurta ni da auren ta. A wannan shekarun na samu Farin ciki, kwanciyar hankali da kuma kulawa na musamman daga gare ta.

Ina mutakar Godiya ga Ubangiji da ya azurtamu da kyawawan yara har guda 3, Al,Ameen, Ayman, da Amatullah. Hakika Sune shaidar soyayyar mu.

A yau ina cikin mutakar farin ciki na soyayyar mu, da kuma duk dawainiyar da take yi da ni da kuma Farin cikin da take saka ni. Ina matukar kaunar ta kuma ina alfahari da ita.

Ina tayaki murna shiga shekara bakwai da Auren mu.

Ina rokon Allah ya kare mu daga dukanin sharri kuma ya karo mana dankon Soyayya na har abada.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA