Labarai

Daga baya kenan : Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

Wata budurwa ƴar Najeriya wacce bata daɗe da haihuwa ba ta bayyana halin da ta tsinci kan ta bayan ta gayawa saurayinta tana da juna biyu.

Ta wallafa wasu hotunan jaririyar ta TikTok da wasu bidiyoyin lokacin da suke tare da mahaifin yarinyar, yayin da take ba jaririyar haƙuri. Jaridar Legit.ng ta rahoto.Daga baya kenan : Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

Jaridar Dimokuraɗiya na ruwaito ta ba jaririyar haƙuri inda take cewa ta samar mata da uba wanda baya ganin darajar ta.

Budurwar ta kuma wallafa hirar da suka yi da saurayin nata inda ya nuna cewa ba shi bane ya ɗirka mata juna biyu.

A yayin da ta nuna irin son da take yiwa jaririyar, ta bayyana cewa tana fatan cewa watarana zai fahimci irin yadda ɗiyar su take.

Daga cikin hirar ta su, saurayin nata mai suna Chima, tun da farko ya ƙi yarda cewa tana ɗauke da ciki, sannan bayan ya tabbatar tana da cikin sai ya ƙi amincewa na shi ne.

Ya gaya mata cewa ta daina takurawa rayuwar sa. Daga ƙarshe dai ta haƙura ta rungumi ƙaddarar ta, inda take cewa tana fatan nan gaba ba zai zo yace yarinyar tasa ba ce.

Ga bidiyon nan kasa ku kalla.

@l_o_m_l_ So sorry baby girl ???? mum loves you so much ❤️ #deadbeatdad #momlife #l_o_m_l #tiktok #goviral #makemefamous #fyp #viral #noticeme #trending #princessbleble ♬ original sound – ShayyBall ☪️Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button