Kannywood

(Bidiyo) Wasu Fusatattun Matasa Sun Cinnawa Gidan Mawaki Dauda Kahutu Rarara Wuta

Yanzu Yanzun nan wasu Fusatattun Matasa Wanda har yanzu ba’a san ko su wanene ba Sun Cinnawa Gidan Mawaki Dauda Kahutu Rarara Wuta da sanyin safiyar nan.

Kamar dai yadda aka sani a Safiyar yau 20 ga watan 3 na wannan Shekara ta 2023 aka bayyana Abba kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben jahar Kano bayan daukar lokaci da akayi kafin Bayyana Sakamakon.(Bidiyo) Wasu Fusatattun Matasa Sun Cinnawa Gidan Mawaki Dauda Kahutu Rarara Wuta

Sai dai tun kafin ranar zabe mawaki dauda Kahutu Rarara tare data hannun damar sa watau Aisha Humaira sun batawa kanawa rai, Sakamakon wata faifan vedio da suka ringa yadawa kan cewa kanawa su zabi Dr Nasir Yusuf Gawuna a matsayin Gwamna.

Hakan ya matukar batawa kanawa rai inda sukaita maida martani harda zage Zage lamarin daya jawo aka kusa bugun Aisha Humaira a ranar da taje kada kuri’ar ta, sai dai bayan wasu awanni jarumar ta bayyana cewa tana cikin koshin lafia babu abinda ya sameta.

Sai dai a Safiyar yau litanin bayan bayyana Abba kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben jahar Kano an samu wasu Fusatattun matasa da suka cinnawa gidan mawaki rarara wuta Al’amarin da ba’a ji dadinsa ba. wanda kuma har yanzu babu tabbacin wanda suka aikata Hakan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button