Auren Soyayya Da Ƙauna Muka Yi Da Sakina Bana Ƙiyayya Ba, – Cewar Aminu Ɗanmaliki
Wani hamshakin dan kasuwa mai suna Aminu Danmaliki mai shekaru 66 ya musanta cewa ya auri karamar yarinya inda yace dan Allah ku ƙyale mu mu ji Ɗadin Auren Mu auren soyayya mu kayi bana ƙiyayya ba.
A tuna cewa, a lokacin da bidiyon bikin ma’auratan ta yaɗu ankafoflon sadarwa, an yi ta sukam auren a shafukan sada zumunta, inda wasu sun kai zargi ‘ Danmaliki da auren yarinya ƴar shekara 11.
Bayan da auren ya janyo cecekufe, angon ya shiga shafin sa na Facebook yana karyata jita-jitar.
A cikin sakonsa na Facebook a ranar Laraba, Mista Danmaliki ya bayyana cewa shekarun matarsa 21 ne, ba 11 ba kamar yadda mutane ke ikirarin.
Ya ce: “Auren da na yi da Sakina kwanan nan ya haifar da tashin hankali da kuma zarge-zarge marasa tushe na cewa na auri yarinya da ba ta kai wuce shekaru 11 ba kuma wai an tilasta mata aure ni.
“Wannan ba gaskiya ba ne. Bidiyon bikin aure ya yi ta yaduwa. Mun yanke shawarar yin shiru amma an shawarce ni da in faɗi gaskiyar lamarin.”
A cewarsa, ba tailastawa matarsa aurensa akai ba, kuma ba a shirya auren ba sai da yardarta.
Ya ce: “Matata akbar kauna ta zaɓe Ni a matsayin mijinta tuta kuma ni ma ina ƙaunarta.
“Ina fata masu mummunan fata da masu ganin ba zai yiwu ba, to dan Allah su kyale mu mu jindadin zaman mu,” in ji shi.