Mataimakin Tambuwal ya sauya sheƙa zuwa APC bayan an yi masa alƙawarin dala miliyan 5
Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Mannir Dan’iya, ya ƙulla yarjejeniyar dala miliyan 5 don sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a yau Alhamis.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi mataimakin gwamnan, wanda a halin yanzu shine dan takarar kujerar Sanatan Sokoto ta tsakiya a jam’iyyar PDP.
Ana sa ran Buhari zai jagoranci gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Sokoto a yau Alhamis tare da gabatar da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, ga al’ummar jihar.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Fabrairu, 2023 kuma ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Kware, mataimakin gwamnan ya ce, “Na rubuto muku sanarwar ficewa daga jam’iyyar PDP daga 8! Fabrairu 2023. Na yaba da damar da aka ba ni, wanda ya sa na yi aiki a mukamai daban-daban a karkashin PDP.”
Sai dai wasu majiyoyi na cikin gida sun ce an gudanar da taro da dama a Sokoto da Abuja tare da shugaban jam’iyyar APC na jihar Aliyu Wamakko da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar a ƙarƙashin uban gidan Dan’iya, Ummarun Kwabo.
“Sun kuma yi alkawarin cewa za a soke shari’ar Mannir da hukumomin yaki da cin hanci idan ya amince ya koma APC gobe,” in ji wata majiya da ta so a sakaya sunanta.