Labarai

Ba Namijin Da Zai Iya Mayar Da Hankalinsa Kacokan Kan Mace -Wani Ɗan Kasuwa

Wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mai suna, Darlington Onyelike, ya shawarci mata da kada su bari soshiyal midiya ta ruɗe su, su yarda cewa namiji da mace daidai da juna suke a aure.

Ba Namijin Da Zai Iya Mayar Da Hankalinsa Kacokan Kan Mace -Wani Ɗan Kasuwa
Ba Namijin Da Zai Iya Mayar Da Hankalinsa Kacokan Kan Mace -Wani Ɗan Kasuwa

Onyelike, wanda ya bayyana hakan a wani rubutu da yayi a ranar Talata, 31 ga watan Janairu, ya kuma janyo hankalin matan aure kan cewa mazajen su ba abokan su bane, saidai iyayen gidan su ne. Shafin dimokuraɗiya na rahoto.

“Babu daidaito tsakanin namiji da mace a aure, ku daina ruɗar da kan ku, ba a yin sarki biyu a gida ɗaya, guda ɗaya ne kawai shine mijinki. Mijinki shine jagora a gidan.”

“Mijinki ba abokin ki bane, ubangidan ki ne. Mafi yawan waɗanda suke cewa sun auri abokan su duk auren su ya mutu. Sannan ba yadda mijinki ya mayar da hankalin shi a kanki har na tsawon sa’o’i ashirin da huɗu, shin ba zai fita yaje ya yayi aiki ya nemo muku abinda zaku ci ba?”

“Hakan na nufin zai tsaya da ke kenan tun daga safe har dare? Ba abu bane mai yiwuwa, mu daina yaudarar kan mu a soshiyal midiya. Ko mara aikin yi ba zai taɓa iya mayar da hankalin sa kan mace har na tsawon sa’o’i ashirin da huɗu ba.” A cewar sa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button