Labarai

Ƙarancin kuɗi: Karuwai sun koka da rashin ciniki a Abuja

Advertisment

A yanzu nan majiryarmu ta samu wani labari mai ban takaici da al’ajabi da ban dariya duba da irin yadda kowa yake ta cikinsa amma su wai karanci kuɗin fata kuke kuka kamar yadda jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito

Wasu karuwai a babban birnin tarayya, FCT, Abuja sun koka kan rashin ciniki a kasuwancinsu sakamakon karancin tsabar kuɗi a hannun kwastomomi.Ƙarancin kuɗi: Karuwai sun koka da rashin ciniki a Abuja

Wasu daga cikinsu da su ka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja a yau Lahadi sun ce ƙarancin tsabar kuɗi na zama barazana kuma ya gurgunta kasuwancinsu.

Sun ce duk da cewa manufar musanya kudi abin yabawa ne, amma yadda ake aiwatar da ita a halin yanzu kalubale ne ga kasuwancinsu.

Advertisment

Karuwan sun ce abokan cinikin su sun ragu sosai saboda halin da ake ciki na rashin tsabar kuɗi.

Sun bayyana yanayin a matsayin abin takaici da tafiyar hawainiya ga kasuwancin su.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button