Yan ta’adda sun kona limamin Cocin Katolika da ransa a jihar Neja
Wasu ƴan ta’adda sun kai farmaki cocin katolika ta St. Peters and Paul Catholic Church, Kafin-Koro a karamar hukumar Paikoro a jihar Neja, inda suka kashe wani limamin cocin mai suna Isaac Achi a cikin gidansa da sanyin safiyar yau Lahadi. Daily Nigerian Hausa na ruwaito.
Rahotanni sun ce ƴan ta’addar sun kona gidan limamin bayan sun kasa shiga cikin gidan da karfi da yaji.
An tattaro cewa wani limamin coci mai suna Father Collins shi ma ya samu raunuka a yayin da ya ke kokarin tserewa daga inda lamarin ya faru.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 3 na asubar yau Lahadi.
Ya ce: “A ranar 15/01/2023 da misalin karfe 0300 ne ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai farmaki gidan wani Rev. Father Isaac Achi na St. Peters and Paul Catholic Church da ke kan hanyar Daza, Kafin-Koro, a karamar hukumar Paikoro.
“Abin takaici, mun samu rahotan cewa ƴan bindigar sun yi yunkurin shiga gidan, amma hakan ba ta samu ba, shi ne su ka banka wa gidan wuta, yayin da Rabaran ɗin ya ce ya kone ƙurmus har lahira.