Labarai

Yadda karuwa ta halaka kanta bayan saurayin da suke harkalla ya yaudare ta ya yi aurensa

Advertisment

An tsinci gawar wata da ake zargin karuwa ce a wani gidan karuwai da ke titin tsohuwar kasuwa da ke Onitsa a Jihar Anambra.

Mamaciyar mai suna Chison daga Jihar Enugu take kuma ana zargin ta rasu ne ranar Litinin, 20 ga watan Janairun 2023 bayan kammala wanke-wanke.kamar yadda Dimokuraɗiya na Ruwaito.

Yadda karuwa ta halaka kanta bayan saurayin da suke harkalla ya yaudare ta ya yi aurensa
Yadda karuwa ta halaka kanta bayan saurayin da suke harkalla ya yaudare ta ya yi aurensa

An yi ta cece-kuce dangane da sanadiyyar mutuwarta a gidan karuwan wanda makwabta da ‘yan gidan suka yi don a kaura, yawanci duk karuwai ne.

Yayin da wasu ke zargin ta rataye kanta a dakin otal dinta, wasu kuma suna zargin halaka ta aka yi sakamakon wani rikici da aka yi da ita kan kudi, yayin da wasu ke zargin guba ta sha ta mutu.

Wata makwabciyarta ta shaida wa The Nation cewa suna zargin ta halaka kanta ne bayan gano wani saurayinta ya yi aure ne ya bar ta.

“Tana da wani saurayi da yake yawan kashe mata kudi. Ko wancan kirsimetin sai da ya kawo mata buhun Shinkafa tare da N200,000 banda sauran kaya da ya kawo mata sannan ya bukaci su yi tafiya saboda kirsimeti daga baya suka dawo.

“Bayan dawowar ne aka sanar da ita cewa ya yi aure. Tun daga nan ne ta dinga yin wasu abubuwa na daban kuma kwana uku da suka gabata aka ganta tana daure hannunta da igiya.

“Yayin da aka tambayeta dalilin rike igiya sai ta fara fada kuma da safe ta share dakinta kusan karfe 9 na safen muka ji ta halaka kanta a cikin dakinta.

“Mun ga wuyanta a daure da igiya da kuma tagar dakinta amma kafafunta suna taba kasa. Don haka ba mu san ko ta halaka kanta bane don mun ga kumfa tana fita daga bakinta yayin da harshenta ke waje.”

‘Yan sanda sun je wurin da misalin karfe 12:30 na rana inda suka dauki gawarta a mota suka wuce da ita.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace ana cigaba da bincike don babu wani rubutaccen bayani da ta yi.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button