Labarai

Wani mutum ya yi garkuwa da mahaifinsa har ya karɓi naira miliyan 2.5 kuɗin fansa

Rundunar ƴan sanda a jihar Kwara da ke yaki da masu garkuwa da mutane ta cafke Issa Naigheti da laifin yin garkuwa da mahaifinsa, Bature Naigboho tare da karbar kudin fansa har naira miliyan 2.5.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ajayi Okasanmi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Ilorin. Daily Nigerian Hausa na ruwaito.

Wani mutum ya yi garkuwa da mahaifinsa har ya karɓi naira miliyan 2.5 kuɗin fansa
Wani mutum ya yi garkuwa da mahaifinsa har ya karɓi naira miliyan 2.5 kuɗin fansa

Okasanmi, mai muƙamin Sufeto na ƴan sanda, ya ce jami’an ƴan sanda sun kama Naigheti a ranar 4 ga watan Janairu a kewayen unguwar Kambi, Ilorin, a yayin da ake bin sahun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

“Ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi cewa ya hada baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo, kuma ya karbi Naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansa.

“Ana ci gaba da kokarin kama sauran wadanda suka aikata laifin, kuma za a mika su zuwa jihar Oyo, inda aka aikata laifin,” in ji Mista Okasanmi.

A Wani labari Ronaldo ya yi suɓutar-baki a Saudiyya

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafar duniya Cristiano Ronaldo ya yi tuntuɓen harshe a lokacin da ake gabatar da shi ga sabuwar ƙungiyar da ya koma ta Al Nassr ranar Talata,

Ronaldo ya yi suɓul-da-baka a gaban magoya bayan ƙungiyar inda ya ce ‘South Afirka’ a maimakon ‘Saudi Arabiya’.

Ɗan wasan ya koma Al Nassr ranar Juma’a bayan da ya raba-gari da tsohuwar ƙungiyarsa Manchester United.

Ronaldo ya ce: “Wasan ƙwallon ƙafa wani abu ne na daban, dan haka zuwana ‘South Afrika’ ba shi ne ke nuna cewa ta-ƙare min ba”

”Wannan shi ne dalilin da ya sa nake son samun sauyi, haƙiƙa ban damu da abin da mutane ke cewa ba”, kamar yadda Ronaldo ya bayyana wa manema labarai a lokacin da aka gabatar da shi a birnin Riyadh.

Ya ƙara da cewa: “Na samu komai, na yi wasa a manyan ƙungiyoyi a Turai, a yanzu kuma lokacin buɗe sabon babi ne a Asiya”.

Bayan taron manema labaran, ɗan wasan ya sanya sabuwar rigar wasansa ta ƙungiyar a filin wasan a gaban dubban magoya bayanta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button