Labarai

Na sha wuta : Ba Gida, Mota, Aiki, Ga Yara Biyu -Wata Bazawara Ta Koka

Wata matashiya ƴar Najeriya, Edi Mac, ta sanya mutane sun tausaya mata a yanar gizo bayan ta bayyana cikin irin halin da take a rayuwa.

Matashiyar ta bayyana cewa, nan da mako biyu masu zuwa zata cika shekara 31 a duniya, amma bata da gida, mota ko ƙwaƙƙwaran aikin yi. Majiyar mu ta  dimokuraɗiya ta rahoto.

Na sha wuta : Ba Gida, Mota, Aiki, Ga Yara Biyu -Wata Bazawara Ta Koka
Na sha wuta : Ba Gida, Mota, Aiki, Ga Yara Biyu -Wata Bazawara Ta Koka

 

Sai dai duk da hakan ta bayyana cewa tana cigaba da yin rayuwarta sannan tayi amanna cewa abubuwa za su daidaita nan gaba.

Matashiyar wacce take da yara biyu, ta kuma ƙara bayyana cewa bazawarace da yara biyu sannan ita take kula da su ba tare da samun wani tallafi daga wajen tsohon mijinta ba.

Duk da hakan ta tiƙi rawa cikin bidiyon sannan ta bayyana cewa taken rayuwar ta yanzu shine ‘ba wahala’.

A kalamanta:

Ina ƙoƙarin nuna cewa komai daidai yake amma a halin da ake ciki nan da mako biyu zan cika shekara 31 a duniya, ba gida, ba mota, ba ƙwaƙƙwaran aiki, bazawara da yara biyu, mahaifin yaran baya tallafawa yaran amma ina cigaba da rayuwata. Taken rayuwata shine ba wahala.”

Mutane da dama sun tausayawa matashiyar inda suka ƙara ƙarfafa mata guiwa.

Ga kaɗan daga ciki:

@Vuyani 2 ya rubuta:

Nayi gidana da motata ta farko ina da shekara 35 a duniya, sannan daga ƙarshe na samun aikin da nake muradi a ina shekara 36. Lamura na sun sauya cikin watanni shida kacal. Ki yarda da ni ubangiji ba zai bar ki hakanan ba.

@Laytesha ta rubuta:

Kakana ya gaya min cewa idan kana da yara, kai mai arziƙi ne.

@Emmaculate Mathebula ta rubuta:

Yau na cika shekara 30 ban taɓa aure ba, ba aiki, ba mota, ba gida ba yara.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button