Labarai

Mutane 18 sun rasu, 40 sun ji raunuka a haɗarin mota a Kebbi

Akalla mutane 18 ne su ka mutu, yayin da wasu 40 su ka jikkata a wani mummunan haɗarin mota da ya afku a karamar hukumar Illela a Jihar Sokoto.

LEADERSHIP ta rawaito cewa haɗarin ya rutsa da wata motar haya ne da kuma motar daukar shanu.

Mutane 18 sun rasu, 40 sun ji raunuka a haɗarin mota a Kebbi
Mutane 18 sun rasu, 40 sun ji raunuka a haɗarin mota a Kebbi

Kakakin rundunar ƴansandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne a mahadar Malisa da ke karamar Hukumar Gwandu a jihar.

Ya bayyana cewa hatsarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata wanda ya shafi direban wata babbar mota mai lamba SRP 442 XA, Jihar Neja da kuma wata mota wadda ta yi jigilar fasinjoji da shanu daga Unguwar Illela zuwa Legas.

Daga nan sai motar ta fadi mahadar Malisa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar shanu 16.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ƴansandan jihar, Ahmed Kontagora ya ziyarci inda hatsarin ya afku, inda ya shaida yadda aka kwashe mutanen zuwa babban asibitin Gwandu inda daraktan kiwon lafiya na asibitin ya tabbatar da mutuwar mutane 18.

Bugu da ƙari, ya ce wadanda suka jikkata suna karbar magani a asibiti.

Kwamishinan, ya yi kira ga masu amfani da ababen hawa da suke bi matakan hanya kuma su kasance masu hankali yayin tuki.

Ya kuma shawarci direbobi da su rika kiyaye ka’idojin tuki sannan su guji yin lodin da ya wuce kima.

CP Kontagora ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma jikansu da rahma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button