Kannywood

Mako ɗaya da rasuwar Kamal Aboki, Mawaƙi Gwanja ya saki sabuwar waƙa “Luwai” da ta hargitsa TikTok

Bayan mako daya da fitaccen dan wasan barkwanci kuma jarumi ga masana’antar Kannywood, Kamal Aboki ya rasu, Mawaki Ado Gwanja ya saki sabuwar waka.

Sanin kowa ne cewa matukar Gwanja ya saki waka sai ta samu shahara fiye da tunanin mai rai ba a Najeriya kadai ba har a kasashen ketare.shafin dimokuraɗiya na ruwaito.

Mako ɗaya da rasuwar Kamal Aboki, Mawaƙi Gwanja ya saki sabuwar waƙa “Luwai” da ta hargitsa TikTok
Mako ɗaya da rasuwar Kamal Aboki, Mawaƙi Gwanja ya saki sabuwar waƙa “Luwai” da ta hargitsa TikTok

A shekarar da ta gabata ne mawakin ya saki wakokinsa masu suna Warrr da Chas. Wadannan wakokin sun yi matukar daukar hankali wanda tuni matan TikTok suka dinga hawa suna gantsare-gantsare da karkada jiki.

Musamman wakar Warr, ya sanya zagi a ciki wanda hakan yasa gwamnatin jihar Kano ta neme shi har da dakatar da siyar da wakar a fadin jihar.

Duk da haka dai ba a dena amfani da su ba domin a fadin jihohin arewa, matukar biki ya yi biki sai an sanya wakokinsa sannan mata ke kwasar rawa.

Bayan wannan ne kuma aka dinga kasa kunne ana jiran jin wacce zai saki a sabuwar shekarar nan, sai ga shi ya saki.

Sabuwar wakar tasa mai suna Luwai ta fara samun karbuwa don tuni mata suka fara hawa suna girgijewa jim kadan bayan ya saki nashi bidiyon yana rawa.

Saidai ya saki wakar ne bayan kwanaki 6 da rasuwar jarumin barkwanci, Kamal Aboki wanda mutuwarsa ta yi matukar girgiza jaruman masana’antar.

Ana tsaka da makoki yayin da malamai ke sakin wa’azi ko ta ina don masu rai su ji su amfana, kwatsam sai ga wannan wakar ta ratsa.

Akwai alamun za ta yi matukar daukar mutane saboda tun yanzu ko ina ya fara daukar zafi mutane na ta bazama neman wakar a yanar gizo.

Kafin kace kwabo, jama’a sun garzaya bangaren sharhi inda suke ta yi masa wa’azi kan mutuwa da kuma tunatar da shi rasuwar abokin aikinsa.

Da fatan jama’a za su gane, su kuma fahimci duniya ba madawwama bace kamar yadda wasu suka bayyana ra’ayoyin su a bangaren tsokaci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button