Labarai

Madallah: Budurwa Ta Ɗauko Tsoho Daga Bakin Titi Ta Nema Masa Matsuguni Mai Kyau

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Julia Nnena, ta faranta ran wani tsohon jami’in tsaro da yayi ritaya ta hanyar kama masa hayar gida mai kyau.

Budurwar ta kaɗu bayan ta ganshi a baƙin titi da ƴan komatsansa, hakan ya sanya ta ji gabaɗaya ta kasa samun sukuni. Jaridar dimokuraɗiya ta rahoto.

Madallah: Budurwa Ta Ɗauko Tsoho Daga Bakin Titi Ta Nema Masa Matsuguni Mai Kyau
Madallah: Budurwa Ta Ɗauko Tsoho Daga Bakin Titi Ta Nema Masa Matsuguni Mai Kyau

A wani bidiyo wanda ya sosa zuciyar mutane da ta sanya a Facebook, Julia taje wurin sa inda ta ɗauke sa zuwa gidan da ta kama masa haya.

Julia ta bayyana cewa, ta ji ba zata yafewa kanta ba idan ta bar shi a bakin titi ba.

Duk da dai ba a kammala sanyawa gidan kayan amfani ba, sabon gidan yana da katifa, gada da ƴan kayan amfanin gida waɗanda zai amfana da su.

Mutumin yaji daɗi sannan ya nuna godiyar sa kan budurwar bisa taimakon da tayi masa. Ya bayyana cewa ya daɗe rabon da ya kwana akan katifa.

Julia ta bayyana cewa mutumin yayi ta ƙoƙarin ganin ya karɓi kuɗin fansho ɗin sa amma abin ya faskara, sai dai bata bayyana wane irin aikin tsaro yayi ba.

“Na yanke shawarar na fara kama masa haya saboda samun fansho ɗin sa zai ɗauki dogon lokaci. An gaya min cewa yana buƙatar wasu takardu. Hakan ya sanya nayi gaggawar kama masa gida yadda zai tada komaɗa ya samun ƙarfin zuwa neman fanshon sa. A cewar ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button