Lauya ya maka CBN a kotu ya kuma nemi a tsawaita wa’adin daina karɓar tsoffin kuɗi
Wani lauya mai suna Joshua Alobo ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ya roki kotun da ta dakatar da babban bankin Nijeriya CBN daga daina karɓar tsoffin takardun Naira daga ranar 31 ga watan Janairu.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito Alobo, a cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/114/2023, ya kuma roki kotun da ta bayar da umarnin tsawaita wa’adin lokacin da tsofaffin takardun za su daina amfani har na tsawon makonni uku.
Ya ce hakan ya kasance don a ba da lokacin da bankunan kasuwanci za su sami isassun sabbin takardun kudi da za su fitar ga al’umma.
A cikin takardar ƙorafin, wacce ya shigar ta hannun Musa Damudi, lauyan ya shaida wa kotun cewa Gwamnan CBN a ranar 26 ga Oktoba, 2022, ya sanar da cewa babban bankin zai buga sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 da aka sake fasalin a cikin tsarin hada-hadar kudi.
Ya ce matakin, duk da cewa an yi maraba da shi, ya haifar da tashin hankali a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman ma masu karamin karfi saboda har yanzu ba su samu damar yin amfani da sabbin takardun kudi na Naira ba.