AddiniLabarai

Kada ka kuskura ka shekara 10 da mace daya – Sheikh Aminu Daurawa

Shehin Malamin addinin Musulunci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shawarci maza da ke son ƙara aure da su yi kafin shekaru 10 da auren farko.

Malam Daurawa ya yi tsokaci ne kan matakan da namiji zai bi don ƙara aure ba tare da tada hankalin uwargida ba.

Kada ka kuskura  ka shekara 10 da mace daya - Sheikh Aminu
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sai dai Malamin ya soma sa bayyana dalilan da yasa mata ke gudun a yi musu kishiya.

“Malam yace shi karin aure abu ne wanda kafin yayi shi ya shirya mishi domin abin karin aure yake nufi shine karin nauyi, karin lokaci ,karin kudin shiga da karin lafiyar jiki da karin gwada cewa mutum zai kwatanta adalci mafi yawan wadanda zasu kara aure basu kallon wadannan bangarorin gudu hudu.

” Malam yace idan kayi shekara goma alaka kana da ‘ya’ya takwas ko 9 da zarar yarka takai shekara goma sha biyar da wuya idan zaka kara aure wadda zaka aure bata wuce shekara ashirin 20 ba ko fiye da haka.

To nan zaka ga wadda zaka auro bata baiwa yarka wasu yan shekaru ba babu wata tazara mai yawa to ita matarka ta samu abokiyar rigima.

“Yanzu za’a iya samu matarka ta tura yarta inda amarya suyi ta kokuwa tana dukan amarya saboda tafi karfinta idan uban yazo yace me wannan uwargida zata ce fadan sune na yara kasani ko kawarta ce ta satar mata pensil a makaranta kasan abin yara

“Duk iya miyar mace duk kwaliyar mace kada ka kuskura kace mata bazaka kara aure ba , domin abinda ke kashe maza kenan idan yaji dadin miya tace ko za’a yi yace ina to ta rike ina din nan sai lokacin da zaka kara aure nan ne zaka ga an wuta sai anyi kusan yakin duniya na ukku”.

Ga cikakken bayyanin nan a cikin Faifan bidiyo ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button