Labarai

Inda Ran ka: Uwa ta kashe aurenta ta auri mijin ƴar ta a Kano

Wani lamari mai kamar wasan kwaikwayo da ya faru a karamar hukumar Rano ta jihar Kano bayan wata mata mai suna Malama Khadija ta kashe aurenta ta auri saurayin ƴyarta.

Majiyarmu ta samu labarin daga Daily Nigerian Hausa cewa lamarin ya faru ne bayan diyar mai suna A’isha ta ki amincewa da mai neman aurenta, inda mahaifiyar ta ce, auran mai neman ‘yarta bai haramta ba a Musulunci.

Tun da farko dai ƴan uwan matar sun shaida wa gidan rediyon Freedom cewa suna zargin kwamandan Hisbah na karamar hukumar Rano da aurar da ‘yarsu ba tare da izininsu ba, kuma ba su ma san inda take ba.

Inda Ran ka: Uwa ta kashe aurenta ta auri mijin ƴar ta a Kano
Inda Ran ka: Uwa ta kashe aurenta ta auri mijin ƴar ta a Kano

Sai dai kuma da take magana da Freedom Radio, Malama Khadija ta ce tana cikin koshin lafiya kuma tana zaune lafiya da sabon mijin nata.

Ta bayyana cewa bayan da ta fahimci cewa ’yarta ta yanke shawarar ba za ta auri mutumin ba, sai ta ji bai kamata su biyu su rasa shi ba, don haka ta yanke shawarar auran mutumin. Ta kuma kara da cewa itama tana da kyau kamar ‘yarta.

Ta ce, “Ban yi auran cikin jahilci ba. Na tuntubi malamai suka ce hakan ba haramun ba ne. Da na tuntubi mutumin kan aure na, ya amince shi amma iyayena da ’yan uwana sun ki amincewa da auran. Hakan ne ya sa na yanke shawarar zuwa Hisbah su daura mana aure wanda yanzu haka, muna cikin farin ciki.”

Kawun Malama Khadija, Abdullahi Musa Rano, ya ce sun ki yarda ta auri mutumin ne sabida da gangan ta kashe aurenta na farko domin ta auri mai neman ‘yarta.

Ya bayyana cewa, “Ta matsa wa mijinta ya sake ta don kawai ta auri wannan sabon mijin na ta. Ba za mu yarda da wannan abin kunyar ba a cikin danginmu. Wannan shine dalilin da ya sa muka ki hada su da aure. Ba mu ji dadin abin da Hisbah ta yi ba, kuma muna ba da rahoton neman ‘yar mu. Muna son babban kwamanda da gwamnatin jihar su shiga cikin wannan lamarin.”

Da aka tuntubi kwamandan Hisbah, Ustaz Nura Rano, ya ce hukumar ta jiha ce kadai ke da damar yin magana kan lamarin.

Da aka tuntubi babban kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Harun Ibn-Sina, ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike kan lamarin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button