Labarai

Hotuna: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare ya dauki hankalin mutane

Allahu Akbar tabbas wannan labarin an tabbar da gaskiyarsa inda yake cewa wannan bawan Allah ya shiga makarantar wajen neman aure kamar yadda wani Fitaccen marubuci a shafin na facebook Saliadeen Sicey na ruwaito

Hotunan Abubakar Muhammad Barinjimi dalibi dan shekara 88 ya dauki hankulan abokan karatunsa da sauran jama’a, yayin da ya shiga aji a makarantar Firamare ta Model ta Hadin Gwiwar Najeriya da Masar da ke Kano, (Nigeria-Egyptian Model School).

Muhammad Barinjimi talaka ne amma yana da kyawawan buri don neman ilimi yayin da yake kusantar shekaru ɗari.

Burinsa dai shine ya yi digiri na uku a ilimin tauhidi.

Dalibai ’Yan uwansa da ke wannan makaranta yawancinsu ‘yan shekara bakwai ne.

An dauki wannan hotunan shekarar 2009 da ta gabata wanda kuma mun samu tabbacin daya gaba cikin malama makarantar ya tabbata da labarin”

Hotuna: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare ya dauki hankalin mutane

Hotuna: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare ya dauki hankalin mutane

Hotuna: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare ya dauki hankalin mutane

Hotuna: Dattijo Dan Shekara 88 Da Ya Shiga Makarantar Firamare ya dauki hankalin mutane

Martanin mutane

Abubakar Jibril yana cewa:

Ni shaida ne domin lokacin ina karantarwa a makarantar sanda ya shigo, Amma bangaren Islamiyya ya shiga 4-6 ba primary ba. Na kasance ina koya ma sa Al-kur’ani mun faro daga suratul Baqara. Mutum ne mai basira sosai domin idan ka biya ma sa sau daya to kuwa zai maimaita ma ka babu kuskure. Har nakan yi ma sa wasa in ce baba ai Duk karatunma ka iya. Yana zuwa tun daga K/Nassarawa zuwa nan Kundila inda makarantar ta ke tare da wasu jikokinsa. Ya rasu ‘yan shekarun baya. Allah Ya gafarta ma sa.

Khaleel Usman Garba yana cewa:

Abubakar Jibril  mun taba haduwa da su a wani program da ake na manta sunan progrm din  a gidan talabijin na CTV wanda yanxu ake kiranta da ARTV ya saka UNIFORM acikin dalibai yara lokacin ina secondry school shekra wajen sha wani abu amma islamiyan mu ce ta dauki nauyin zuwan namu

Musaddeeq M Abdullahi yana cewa :

Still Ma lokacin muna secondary school. Akwae Dattijo Wanda yake karatu ‘a makarantar S.A.S, Sauran Dalibai sunci Albarkacin sa, Domin makararru Jira Suke ya karaso su shiga makaranta tare.
Su Kuma malamai gani suke duk Daliban makararru ne, Idan aka Hukunta wani aka bar wani Anyi rashin adalci. Shi Kuma baba bazai Hukuntu ba.
Saboda haka Sai su Bari kowa ya wuce Aji babu Hukuncin makara, Albarkacin Baba.
Haka akayi Har Ya rasu

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button