Garin Daɗi: yadda budurwa ta nuna sauyin cigaba a rayuwarta bayan tayi wuff da wani bature
Wata matashiya baƙar fata mai suna Ruth Njau, ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna irin sauyin da ta samu bayan tayi wuff da wani bature farar fata.
A cikin ƙayataccen bidiyon, ta bayyana cewa baturen mijin nata ya sanya rayuwarta ta samu gagarumin sauyi bayan sun yi aure. Jaridar dimokuraɗiya ta rahoto.
Ta kwatanta irin rayuwar da take yi a baya da kafin ta haɗu da mijinta da kuma irin daular da take ciki a yanzu bayan ta yanke shawarar suyi rayuwar aure tare.
A cikin bidiyon na tuna baya, an nuna ta tana ta aiki tuƙuru tana ɗebo ruwa a rijiya domin cika wasu tulin jarkoki.
Bidiyon ta na halin yanzu ya nuna ta tana rayuwar watayawa ita da baturen mijinta a cikin wata mota mai ɗan karen tsada.
Ku kalli bidiyon a nan
@ruthnjau #ruthnjau ♬ original sound – Masego????
Mutane da yawa sun yi sharhi akan bidiyon, inda suka yi ta taya ta murnar cewa kakarta ta yanke saƙa.
Martanin Mutane
Bloom ta rubuta:
“Wannan gagarumin sauyi ne.”
@daddythurayya ya rubuta:
“Wannan labari ne mai daɗin ji. Allah ya albarkaci tarayyar ku.”
@Ginaegbe190 ta rubuta:
“Nan a ina wani sauyi yake?”