Datti Assalafy yayi Martani Mai Zafi kan wadannan Hotunan Rahama Sadau
Fitaccen marubuci nan Datti Assalafy yayi wa rahama Sadau wankin babban bargo akan wallafa wasu sababbin hotuna da tayi a wani sabon salo da ta bayyana a shafukansu na sada zumunta ga abinda yake cewa.
“MASU KOYAR DA TARBIYYA
Shahararriyar jaruma a masana’antar Hausa film Rahama Sadau ta saki wasu zafafa hotuna na fitsara da gashin doki a kanta domin matan Musulmi suyi koyi da ita
Jama’a wadannan sune karnukan farautar Yahudu da nasara wadanda ake cewa suna koya mana tarbiyya da fadakarwa a Kasar Hausa
To kunga irin tarbiyyan da kuma fadakarwan, ko wacce bata da addini ne tayi irin wannan shiga za’a iya cewa ta fitsare, balle Musulma da aka haifeta cikin Musulunci
Na tabbata kafin Rahama Sadau ta shiga Hausafilm ko nawa za’a bata ba zatayi irin wannan shigar ba, amma kunga abinda shiga masana’antar Hausa film ya kai ta ya baro tana ‘yar Musulma
Kuyi hakuri da ganin hotunan, muna sakawa ne domin ya zama hujja kar a zargemu cewa sharri muke musu, kuma mun damu da su ne saboda ance masu koya mana tarbiyya ne, amma abinda muke gani masu lalata mana tarbiyya ne
Duk Musulmin da ya wayi gari ya ga ‘yar sa tayi irin wannan shigar abinda zai fada a ransa shine ko tayi ridda ne?, don ko ‘yar isk@ ce Musulma tayi irin wannan shiga sai ta bada mamaki
Allah Ka shiryar da ‘yan Hausa film, Ka kare Musulmai daga sharrinsu اللَّهم آمين”