Bidiyon matashin da ya yi ankon suttura da kare, ya sanya shi a gaban mota ya ɗauki hankula
A wani guntun bidiyo, an ga yadda wani matashi da kare suke kwasar rawa a cikin wata mota yayin da suke sanye da suttura iri daya.
Dimokuraɗiya na rahoto labarin yayin da wata waka ke tashi, an ga yadda mutumin ke kambama karen yayin da karen ya cigaba da gyada kai ga kidan.
Mutane da dama sun yi mamaki yayin da suka dinga tsokaci kan yadda karen ya dinga yin abubuwa kamar mutum.
Wani @love_n_nazhas ne ya wallafa bidiyonsa da karensa a TikTok yayin da suke duk harkoki iri daya a cikin motarsa.
@love_n_naz #abidjan225???????? #cotedivoire???????? #ivoiretiktok #ivorycoast???????????????? #congolaise???????? #congo #zaimustaa #ambiance #ambianceur225 ♬ original sound – love_n_naz
@love_n_naz♬ original sound – love_n_naz
Tabbas saka kaya iri daya da suka yi ne ya fi komai daukar hankali kuma yadda karen ya ke bin salon wakar tamkar ya san abinda ake cewa.
Akwai wani wuri a bidiyon wanda aka ga karen ya juya kan sa zuwa tagar motar yadda mutane su ke yi.
Zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tattara tsokaci fiye da 6,000 yayin da fiye da mutane 140,000 suka yi jinjina kan bidiyon.