Labarai

Bari ba shegiya bace : Samarina sun gujeni bayan sun dirmamin ciki – wata budurwa ta koka

Wata budurwa ta koka kan yadda maza daban-daban suka ɗirka mata ciki, suka gudu suka bar ta da rainon yara.

Budurwar mai shekara 23 a duniya ta bayyana cewa tana da yara uku yanzu haka, kuma kowanne daga cikin su mahaifin sa daban. Jaridar dimokuraɗiya ta rahoto.

Bari ba shegiya bace : Samarina sun gujeni bayan sun dirmamin ciki - wata budurwa ta koka
Bari ba shegiya bace : Samarina sun gujeni bayan sun dirmamin ciki – wata budurwa ta koka

Budurwar ta dai bayyana wannan abin taƙaicin da ya faru da ita ne a wani bidiyo da ta sanya a manhajar TikTok.

A cikin bidiyon wanda take ta sharɓar kuka, ta bayyana cewa a cikim watan Fabrairun wannan shekarar zata cika shekara 24 a duniya, amma har yanzu aure ya gagare ta.

Ku kalli bidiyon a nan

@shemabby♬ son original – richtogo

Bidiyon na ta ya ɗauki hankulan mutane sosai, inda sama da mutum dubu ɗari biyar suka kalle shi, sannan wasu da dama daga cikin su suka riƙa ƙarfafa mata guiwa da bata shawarwari.

Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin mutane waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:

crowns225 ya rubuta:

Kada kiyi kuka, ƴaƴa kyauta ce daga Allah, ba komai bane da kake so kake samu, ki cigaba da addu’a komai zai daidai.”

user1904033585248wamboz ta rubuta:

“Kada ki damu, ba dole bane sai kin yi aure sannan yaran ki za su rayu.”

Ur ex girlfriend ta rubuta:

“Eeeiiii Maame ni da zan cika shekara 29 wata mai zuwa bana kuka saboda hakan. Ki mayar da hankali kawai wajen samun kuɗi sannan ki ƙauna ci kan ki.”

user199930381305 ya rubuta:

“Ki yi haƙuri kin ji, ki roƙi ubangiji zai kawo miki nagari wanda zai zama uba ga waɗanda kike da su yanzu.”

marymercy49 ta rubuta:

“Wannan shekarar zan cika shekara 28, ina da yaro wanda ni kaɗai nake kula da shi, ki zama jajirtatta kawai ƴar’uwa ta.”

awuramafosuah ta rubuta:

“Wani yana can yayi aure amma baya da yaran da kike da su, ki zama mai godiya yar’uwa.”

k ta rubuta:

“Shekara ta 26 ba saurayi, ba ɗa, ba aikin yi kai banda komai…amma ta yaya akai kika samu waɗannan yaran kowanne uban sa daban.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button