Labarai

Bankuna sun ci Amanarmu akan sababbin kudi – CBN ya koka

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce ya ji takaicin yadda abubuwa ke tafiya, yana mai cewa ana amfani da sabbin takardun Naira a wajen sharholiya. Kamar yadda Dimokuraɗiya ta ruwaito.

Ya ce hakan ya nuna cewa bankunan kasuwanci sun karya umarni da ka’idojin da CBN ya ba su.

Bankuna sun ci Amanarmu  akan sababbin kudi - CBN ya koka
Bankuna sun ci Amanarmu akan sababbin kudi – CBN ya koka

Emefiele ya bayyana hakan ne yayin da yake karin haske kan sabuwar manufar kudin a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai a ranar Talata.

Ya ce babban bankin ya sake tabbatar da kudurin sa na shigar da dukkan hukumomin tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa wajen damke masu yin zagon kasa ga wannan manufa ta canza kudi.

Ya kara da cewa fa’idar amfani da kasuwanci ta hanyar fasahar zamani wato te-economy ya fara bayyana yayin da aka rage samun hauhawar farashin kaya.

Ya kuma kara da cewa, an dan takaita sace-sacen mutane don neman kudin fansa da sauran laifuffuka domin wadanda suka ci gajiyar wannan aika-aika ke da wuya su tattara ko kwashe kudadensu na haram daga wadanda abin ya shafa ko kuma iyalansu (wadanda aka yi garkuwa da su).

Ya ce ko da yake wasu ’yan Najeriya na iya shafan wannan tarnaki.

A wani labari kuma, Yanzu-Yanzu: Kocin Wikki Touriats Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Kabiru Dogo ya yi murabus daga mukaminsa na babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourists.

Dogo, DAILY POST ta samu labarin cewa ya mika takardar murabus dinsa ga mahukuntan kungiyar ta Bauchi Elephants a yammacin ranar Talata.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button