Labarai

Banjin Daɗin Aure Matata Ta Hana Muyi Kwanciyar Aure – miji ya koka

Wani magidanci ɗan ƙasar Kenya mai suna James Jkorir ya koka kan yadda matar sa take hanawa suyi kwanciyar aure.

Magidancin ya bayyana cewa yayi nadamar auren matar sa saboda duk lokacin da ya nemi da suyi kwanciyar aure ta fake da cewa bata da lafiya. Shafin dimokuraɗiya ta rahoto.

Banjin Daɗin Aure Matata Ta Hana Muyi Kwanciyar Aure - miji ya koka
Banjin Daɗin Aure Matata Ta Hana Muyi Kwanciyar Aure – miji ya koka

Magidancin ya nuna ɓacin ran sa ne dai a wani rubutu da yayi a wani dandali na mabiya addinin Kirista, a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.

A kalaman sa:

“Ya zanyi da matar da take ƙaryar bata da lafiya duk lokacin da na nemi muyi kwanciyar aure. Nayi nadamar kasancewa cikin wannan auren!!!”

Mutane da dama sun mayar da martani akan wannan maganar da magidancin yayi, inda da yawa daga ciki suka bashi shawarwari kan yadda zai shawo kan matsalar.

Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:

Israel Lawson ya rubuta:

Ko dai baka san yadda ake yin aikin ba ko kuma kana ji mata ciwo ne. Ka zauna ka nutsu da kyau ka gano menene ba kayi daidai, sai ka zaunar da ita kayi mata alƙawarin cewa zaka gyara sannan kayi ƙoƙarin ganin ka gyaran.

Grace Wambui Waturu ta rubuta:

Wannan matsalar rashin tattaunawa ne. Ko da yaushe ina cewa bai kamata ma’aurata na ɓoye junan su wani abu ba.”

Yitzhak Babu ya rubuta:

Matar ka ce. Kada kaji komai kayi mata magana kaji meyasa take yin hakan. Ka gaya mata yadda kake ji idan tayi hakan. Ta iya yiwuwa akwai yadda take son ayi aikin amma ba kayi daidai. A ɓangare ɗaya kuma ƙila tana samun abinda take so ne a wani wajen amma kada kayi saurin yanke hukunci ba tare da samun hujja ba”.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button