Ba zama: Yadda ɓarawo ya saki matar mai gida
Wani malami wanda ya shahara a wajen rubuce rubuce masu fadakarwa sukairaj Hafiz Imam ya kawo wani labari mai matukar ban tausayi amma kuma akwai darirya a cikin wannan labarin.
“Ya dawo gida y samu matarsa tana ta sheƙa kuka. Ya tambayeta ko lafiya? Ta yi masa banza! Shi dai kawai yaga tana haɗa kayanta.
Suna cikin wannan halin sai ga Babarta da Ƴan uwanta sun shigo… Ya tambaye su cikin damuwa da mamaki ko me yake faruwa…?
Mahaifiyarta ta ce, ka saki yarinyar sa’annan ka tambaye ni me yake faruwa saboda rainin wayo..!
Ya ce, sam bai saki matarsa ba. Aka nuna masa saƙon kar ta kwana da ya turo na sakin.
Sai ya ce, ɗazu aka sace wayarsa, da alama wanda ya sace wayar ne ya turo da wannan saƙon.
Ya karbi wayar matar ya kirawo barawon ya ce, bayan rashin adalcin sacen wayar da ka yi kuma sai ka haɗa da zalincin sakar mini mata..!
Barawo ya ce, tun da na ɗauki wayarka nake ganin matarka tana turo da saƙwanni daban-daban, in zaka dawo gida ka siyo Dankali, bayan ɗan lokaci ta sake turo wani saƙon ka siyo Nama, wani saƙon ka siyo albasa…….
Saboda ban bata amsa ba ta kirawo waya tana ta masifa, shi ne naga bari na rage yawan zunubin da na aikata na satar wayarka ta hanyar fitar da kai daga ƙangin matarka don kar dukan ya zama biyu.”