Labarai

Ba za mu ƙara wa’adin amfani da tsoffin kuɗi ba – CBN

Advertisment

Babban bankin Najeriya CBN ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfanin da tsoffin takardun kuɗin ƙasar daga ranar 31 ga watan Janairu.

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka bayan ganawar kwamitin babban bankin kan tsare-tsaren kuɗi.

Gidan jaridar Bbchausa na ruwaito Mista Emefiele ya jaddada cewa babban bankin ya bayar da wadataccen lokaci ga ƴan ƙasar da su mayar da tsoffin kuɗadensu zuwa bankunan ƙasar domin musanya su da sabbi.

Gwamnan babban bankin ya ƙara da cewa tun bayan sauya fasalin takardun kuɗin uku an samu raguwar garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Ba za mu ƙara wa'adin amfani da tsoffin kuɗi ba - CBN
Ba za mu ƙara wa’adin amfani da tsoffin kuɗi ba – CBN

Ya ƙara da cewa kawo yanzu babban bankin ya karɓi tsoffin takardun kuɗi da adadinsu ya kusa naira tiriliyan 1.5, tare da fatan cewa za su iya kai wa tiriliyan biyu kafin cikar wa’adin da bankin ya saka.

”Mutane na ci gaba da riƙe kuɗi tare da ajiye su a gidajensu, alhalin ba su da izinin yin hakan, kuma suna amfani da su wajen yaɗa jita-jita game tsoffin takardun kuɗin” in ji Emefiele.

Ya ci gaba da cewa: “Mun roƙi Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC da hukumar yaƙi da almundahanar kuɗaɗe ta ICPC da kada su matsa wa mutane, kuma bisa alfarmar da na roƙa ba za su yi hakan ba”.

Ƴan Najeriya da dama na ƙorafi game da ƙarancin sabbin takardun kuɗin, suna masu cewa har yanzu bankunan ƙasar na bai wa kwastomominsu tsoffin takardun kuɗi a yayin da ya rage ƴan kwanaki kafin ƙarewar wa’adin da babban bankin ya bayar ya cika.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button