Ba Sha’awa ke sa Gabanki jikewa ba – binciken masana
Ba maza kadai ke iya fahimtar lafiyar al’uransu ba. Kamar yadda muka yi darasi a baya na yadda duk safiya ko yadda gaban maza yake mikewa idan suna bacci. Kamar yadda shafin Abdul U tonga mai makarantar tsangayar malam na ruwaito.
Suma mata sunada hanyar da suke iya gane suna cikin koshin lafiya musamman ta bangaren farjinsu.
Sau tari wasu matan suna kokawa na yadda gabansu yake jike a kullum. Wasu matan na daukan hakan tamkar wata lalurace ko kuma yawan jaraba ce na son Jima’i, sam abun ba haka yake ba a cewar masana.


Shi gaban mace mai lafiya a kullum ana son ganinsa yana cikin naso da kuma danshi. Wannan ne yake tabbatar da mace na cikin koshin lafiya a bangaren al’auran ta, kamar yadda masana suka tabbatar.
Wannan ruwan da yake jika gaban mace ba yana nufin tana da karfin sha’awa bane. Sai dai ruwane da yake wanke duk wani abu mara kyau da zaran ya shigeta.
Da yake Allah Ya halicci gaban mace a bude, hakan na iya sa cuta ya shigeta cikin sauki. Da wannan ne sai Allah Ya mata wani ruwa na daban daga jikinta da zai riga wanke mata gabanta lokaci zuwa lokaci ba tare da sai tayi amfani da ruwa ko sai a lokacin data zo tsarki ba. Ganin cuta na iya shiga gaban mace a kowani lokaci, sai Allah Ya hukunta aikin wannan ruwan gaban mace a kowani lokaci cikin awanni 24.
Mata masu karancin shekaru sunfi ganin gabansu a jike a koyaushe. Hakan na kasancewa ne saboda yadda jinin jikinsu yake da lafiya da kuruciya. Sannan kuma basu samun wadatar yin Jima’i kamar yadda mace mai aure take samu. Domin yawan Jima’i yakan rage fitowar wannan ruwan a gaban mace. Hakan nan idan mace shekarunta ya soma ja, ita ma ba safai za a rika ganin hakan daga gareta ba sai idan mace mai halice tana samun abincin da suke kara ni’ima sosai tana ci ko sha.
Masana sun hana mata amfani da foda ko turare a gabansu. Domin gaban mace bai bukatar wani ruwa ko sinadarin daga waje domin ya wanke shi. Wannan ruwan dai dake fitowa a jikinki shine ruwan dake kula da tsaftace gabanki da kuma yakar duk wata cutar data tinkaro gabanki.
Don haka matan masu damuwa saboda yawan jikewa da gabansu yake yi su daina damun kansu. Lafiyane suke da shi. Haka kuma ba domin wannan ruwan ba da sun rika fama da cututtuka.
Shi yasa masana ke baiwa mata shawara su rika amfani da ruwan dumi wajen yin tsarki maimakon ruwan sanyi. Domin ruwan dumi na kara taimakawa wajen kashe cutukan dake gaban mace.
Yana kuma da kyau mata su rika amfani da kamfen da aka yisu da auduga wato cotton fabric underwears domin sun fi dacewa da kula da lafiyan gabansu maimakon sauran yadukan.
Ruwa a jiki da gaban mace. Shi yake sa ta zama mace. Duk macen dataga tana bata kayanta, kada ta dauka jarabace da ita lafiyace. Sai dai daga lokacin da taga ruwan ya sauya launi kuma yana wari ko karni. Tayi maza ta tuntubi likita.