Labarai

An kama Kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da ya damfari wani dattijo naira miliyan 250

Advertisment

 

Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar Ƴan Sanda ta jihar Legas, ta kama wani Oluwole Akande, dan shekara 55 da haihuwa, bisa zarginsa da laifin yin basaja a matsayin kwamishinan ƴan sanda, CP Yetunde Longe, ya kuma damfari wani tsoho mai shekaru 80 naira miliyan 250.

An kama Kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da ya damfari wani dattijo naira miliyan 250
An kama Kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da ya damfari wani dattijo naira miliyan 250

Daily Nigerian Hausa na ruwaito cewa Kwamishinan, na yankin railway, CP Yetunde Longe, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa kama wanda ake zargin a jiya Laraba a Legas.

Longe ta ce ta samu kira daga CP Frank MBA, tsohon mai magana da yawun rundunar kan lamarin.

Ta ce matar wanda ake zargin ta kira Mba domin ta tsegunta masa shirin da wani CP Longe ke yi na neman mijin nata ya bashi miliyoyin Naira, domin ta kashe maganar wata kara da a ka kai mata a kan mijin ta.

“CP Frank Mba ya amsa wa matar wanda abin ya shafa cewa ya san CP Yetunde Longe ba za ta yi irin wannan mummunar bukatar ba, ya yi alkawarin zai kira ta ya tabbatar ya dawo wurin matar.

“CP Frank Mba ya kira ni don in ba da labarin lamarin kuma na tabbatar da cewa bayanan ba daidai ba ne. Na ce babu wani koke a gabana kuma ban ma san wanda abin ya shafa ba.

” A wannan lokacin ne aka sanar da CID Panti na jihar domin gano wanda ake zargin kuma an kama shi. Ya furta cewa ya kwaikwaye ni,” in ji Longe.

Kwamishinan ta ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button