An ɗaura Na zama matar Abba, Allah Nagode maka, Bidiyon amarya cike da farinciki mara misaltuwa
Wani bidiyo ya yi matukar daukar hankalin mutanen shoshiyal midiya bayan ganin wata amarya cike da farinciki mara misaltu.
A bidiyon wanda take sanye da kaya launin farare da alamu ranar aurenta ne ya dauki hankali, shafin Gaskiya zalla na Instagram ya wallafa.
A bidiyon an ga yadda ta kasa boye farincikinta inda ta kwashi rawa tana daga hannunta sama tana godiya ga Ubangijin da ya nuna mata ranar aurenta.
Ko da gani tana matukar kaunar angon nata mai suna Abba wanda hakan yasa ta kasa boye murnar. An ji tana cewa:
“An daura an daura, na zama matar Abba. Allah Nagode maka.”
Martanin Mutane
@hajjasalmacollectionlagos:
Dan Allah anemomana abba mugansa
@xeedamulky :
@hajjasalmacollectionlagos wlhy nima zan so naganshi????
@beentuameen cewa take
MashaAllah Allah ya dauwamar muku da farinciki
Wannan bidiyon ya dauki hankali sosai. Wasu na ganin rashin kunya ne tayi. Inda wasu kuma ke ganin tsabar siyayyar da ke tsakaninta da angonta ne ya janyo hakan.
[Via]