Amarya ta rasa Ido ɗaya ana tsaka bikinta sakamakon duka da ‘yan ƙato da gora suka mata
Wata Amarya mai suna Khadija Abdullahi ta makance a ido ɗaya sakamakon zabga mata gora da ‘yan ƙato da gora suka yi
Wannan ibtilain dai ya faru da Khadijah ne ana tsaka da shaglin bikin ta a unguwar Ɗantamashe da ke Kano.
A cewar Khadija Ƴan kungiyar sintiri na Vigilante na unguwar su ka yi mata wannan aika-aikan lokacin da suka zo raraka ana tsaka da kidan DJ
Khadija amarya tana cewa
“Ni wanann abun kiyaya ce ni bansan yadda zanyinda rayuwata ba.
Ni bansan wanda yayimin aikin ba nidai na farka naga kaina a asibiti
Khadija ta kara da cewa tabbas wadanda ake zargi sune domin sunzo da ariyisu su da yawa sosai wanda har kina waya suke suna cewa a karo musu wasu mutane daga cikin yan kwamitin su.”
Ga dai cikakken bayyanin nan daga bakin amarya mai ido daya.