Labarai

Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

A yau Laraba ne dai ɗan Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata
Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

Daily Nigerian Hausa ta ruwai cewa Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano.

Ya bayyana cewa sun haɗu da marigayi Ummita ne a 2020, bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi.

Jaridar Justice Watch ta rawaito cewa ɗan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta riƙa karɓar kuɗaɗe a wajen sa, ya ƙara da cewa ” haka na riƙa bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na ɓata mata rai. Ma kashe mata kimanin Naira miliyan 60,”

Ya ƙara da cewa har gida na miliyan 4 ya sai mata, amma sai ji yayi ta yi aure, bar hakan ya ɓata masa rai ya koma Abuja da zama.

“Amma duk da haka ta riƙa kira na tana hira da ni ta WhatsApp. Bayan nan ta ce min auren ya mutu, shine soyayyar ta mu ta dawo,”

A cewar sa, wata rana ta tambaye shi kuɗi shi kuma ya ce bashi da shi, shi ne Ummita ta yi fushi da shi har ta deba kula shi.

“Kawai sai ta ce min ta samu wani saurayin, har ma ta turo min hoton ta da shi sabon saurayin nata, lamarin da ya fusata ni,” in ji shi

Alƙalin kotun, Sanusi Ado Ma’aji, ya bada umarnin a ci gaba da tsare Quanrong a gidan yari, sannan ya ɗage zaman zuwa gobe Alhamis domin ci gaba da sauraron kariya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button