Labarai

Zamu Dinga Biyanka Miliyan Biyar N5Million duk wata idan zakayi mana aiki Atheist (yada da’awar Rashin akwai Allah)

Na gamu da wani Bawan Allah ta wannan shafi na Facebook mai suna Abu Hanifa Assalafiy, wanda ya dade yana bibiyata Dan bu qulla Abota dashi, Duk da ya kasance mazaunin Kaduna ni kuma ina Kano.
Yazo guna Har sau biyu, Duk lokacin da zai zo zaizo da shiga ta kamala , kuma yana zuwa ranar juma’a Har muje Tafsirin na Dr. Muhd Sani Umar R/lemo tare shi.
Zamu Dinga Biyanka Miliyan Biyar N5Million duk wata idan zakayi mana aiki Atheist (yada da'awar Rashin akwai Allah)
Galibin hirar da muke dashi akan Addini ne , saboda dama Rubutun dake yi Akan addini yafi yawa .
Ya nemi nazo kaduna dan na kawo masa ziyara.
Bayan na yanke shawar zan ziyarce shi zuwa garin kaduna , sai kuma tafiya ta kamani wanda na Bar Qasar Nigeria Har na dau wajen shekaru Hudu.

Na sanar dashi Bayan Nabar Nigeria, Amma bai nuna damuwar sa ba, muka cigaba dazumuncin mu.
Indai nayi magana Akan “yan shi’a ko Audu filin mushe Abisa wata Katubara da yayi, zamuyi ta tattaunawa dashi , ya na nuna min damuwar sa Qwarai da gaske akan yadda , “yan acabar malamai , ko ince “yan aruftan malamai suke yiwa Addini hawan qawara.
In taqaice maka labarin Bayan na dawo Nigeria Wannan bawan Allah sai ya Qara nemana da Nazo Garin Kaduna.

To saboda matsalar tsaro da ake fama da Ita , na gaya masa gaskiya bazan iya zuwa ba. Har muka yi wasa da dariya , yana tsokanata “idan ma an sace ka wlh ko nawa ne zamu biya kudin fansa ” nayi dariya nace Allah ma ya kiyaye.
Katsam Rannan Sai ya bugumin waya yace zasu zo kano shida wasu Abokan sa, kuma sabo dani zasu zo , idan sun shigo zasu kira ni.
A wannan lokacin kuma ni ina Bauchi, sai yace to babu damuwa idan na dawo na sanar dashi.
Bayan na dawo, na sanar dashi , suka sanya lokacin zuwa Suka zo .

Sai dai tundaga lokacin da suka zo Sai naga duk Abu Hanifa Assalafiy ya canja, wajan sanya tufafinsa da maganganun sa , ba kamar yadda nasan shi A baya ba. Kuma sunzo su hudu, dukkan su samarine , Amma da manyan motoci guda Biyu.
Kuma zuwansa biyu dayayi duk ranar juma’a ne harmuje karatu dashi, Amma wannan zuwan sai suka zo ranar Talata.
Idan nayi masa maganar Abunda ya shafi Addini sai naji yace , kai kabar wannan maganar Alaji. Ba kamar da ba , yadda yake nuna damuwar sa.

Abun ya fara bani mamaki, wanda ni yana kirana ne da ya sheik, Amma yanzu naji yana cemin Alaji.
To Amma banyi mamaki ganin haka ba saboda tsahon lokaci da muka dauka bamu hadu ba , na san komai zai iya canjawa acikin hsekaru hudu.
Muna dai ta hirar irin Abubuwan da suke faruwa a duniya.

A qarahe sai yace min Ibrahim Dawud wata magana muka zo maka da ita wacce zaka samu mahaukatan kudi, fiye da yadda baka zato , kuma ba komai ne yasa ba saboda munga yadde kake da qoqari wajen jajirciwa a Media, da wayar da kan Al’umma akan Addini.
wlh tunda ya fadi wannan magar , sai Kai na yabuga , azuciya ta nace Allah yasa wadannan mutane ba cutar dani zasuyi ba. Domin yardar da nayi dashi. Ko kuma su jefani cikin wata halaka, duba da yadda rashin tsaro ke taka rawa a yanzu.

Kuma gashi naga ya canja ba yadda nasan shi a baya ba.
Sai gabana ya fara faduwa, Na fara neman tsarin Allah daga garesu.
Sai suka bijirumin da Tallan , Atheist (wadan da basu yarda da samuwar Allah ba).
Sukace za a dinga biyana Naira miliyan 5 , duk wata. Za a bani Computer da Babbar waya wacce zan dinga Amfani da ita, kuma zan fadi duk inda nake so abani gida , inda kawai zan zauna ina yada wannan Aqida.
Kuma zan bude wani Account A Facebook Ba wanda nake Amfani dashi ba, dan kada ma mutane su gane nine.
Mun dau tsahon lokaci dasu, Suna nunamin Rashin kasancewar Akwai Allah, Amma cikin yarda Allah da taimakon sa , Allah ya kubutar dani.

Na ga Abun dagaske suke , kuma kada su cutar dani dan bansan suwaye iyayen gidan suba , sai nace zanyi shawara.
Bayan munrabu dasu , na juya baya zan tafi, sai shi Abu hanifa Assalafiy, ya kirawo ni, yace na bashi Account Number ta, sai nace A’A adai bari nayi shawara, yace to shike nan sai yajini , nan mukayi sallama.
Tunda na dawo gida , na kasa bacce jikina yana ta karkarwa, Amma ina ta fadin innalillahi’wa’inna’ilaihirraji’un.
Ban samu nayi bacce ba , na diga roqon Allah da ya tsareni daga sharrin wadan nan mutane.
Saboda ni ban taba shiga musifa da takai wannan ba.
Wannan dalilin ne yasa na rage yawan rubutu a Facebook. Saboda razanin da na shiga ciki a wadan nan kwanaki.

Yau wata uku kenan da faruwar wannan abun na kasa gayawa kowa, Abunda yasa nayi wannan rubutu saboda naga wani shima yayi bayani akan kusan abunda ya sameni, shi kuma Abu Hanifa naga Shafinsa na Facebook ya canja shi ya koma chale Michael, mutane su dage da Addu’a, saboda nasan idan wani ya tsira , wani bazai kubuta ba , saboda Ana Amfani da Kudi saboda ansan Akan su babu abunda baza a iya ba.

Shi kansa Abu Hanifa Assalafiy, ina zaton abunda ya ja shi ke nan. kuma kasan kwai wadan da suka daure musu gindi dan yadda wannan Aqida, kuma yadda aka zubawa harkar kudu , wlh kasan akwai matsala.
Sai dai kawai Allah ka tsare mana imanin mu ka , tabbar damu Akan sunnar Annabin ka. s.a.w., ka tsaremu daga duk wasu fitintinu na rudun duniya ya Hayyu ya Qayyumu.
Ibrahim Dawud Abdulhamid
01-03-2022.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button