Labarai
Yan matan Najeriya munana ne, ban taɓa ganin kyakkyawa ba – Matashi
Wani dan asalin kasar Uganda dake zama a California, A.J Ssesanga ya ce bai taba ganin kyakkyawar mace ‘yar Najeriya ba, LIB ta ruwaito kamar yadda dimokuraɗiya na wallafa
Ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, karkashin wata wallafa a Twitter wacce ake lissafo jerin kasashen Afirka masu kyawawan mata.
A jerin an lissafo kasashen inda aka fara da kasar Ghana, Tanzania, Najeriya, Uganda, sannan Afirka ta Kudu.
Ganin hakan ne A.J ya yi gaggawar bukatar a cire Najeriya daga jerin kasashen saboda a cewarsa shi dai har yau bai gamu da kyakkyawar mace ba ‘yar Najeriya.