Yadda Zaka Gane Bada Kaikadai Take Soyayya Ba
Mata sunada wata al’ada na tara samari. Wasu matan suna yin hakan ne saboda kodayin abunda zasu rika fizga daga wajen masu sonsu. Wasu kuwa a cewarsu suna hakan ne saboda rashin tabbacin gaskiyar masu zuwa nemansu.
Sai dai koma wani dalili ne cikin biyun nan mace take tara samari hakan yana iya zamemata illa a rayuwarta tana sane ko kuma a rashin sani.
Smari ga wasu alamun da muddin ka fahimci wacce kake nema da aure tana makasu, babu makawa karya take maka ba Kaikadai bane saurayinta.
1: Kin Gabatar Da Kai Ga Makusanta:
Duk budurwan da kake soyayya da ita amma kaga taki ta gabatar da kai ga makusanta ta irinsu kawayenta, kannenta ko yayyunta. Kawai ka ja jiki bata kai take ba.
Domin ita macen datake sonka abu na farko da zata soma yi shine taga makusantanta sun sanka. Hakan kuma zai yi wuya bayan ta gabatar da kai ta sake gabatar da wani muddin wannan gidan akwai tarbiya.
Idan har kana soyayya da mace kuka haura watanni bata nunaka ga makusanta ba, gaskiya ba da kai kadai take soyayya ba. Kila akwai abunda take amfana ne daga gareka.
2:Bata Cika Damuwa Da Kai Ba:
Alamu na biyu da zaka iya fahimtar ba Kai kadai kake soyayya da mace ba shine rashin nuna maka kulawa.
Sau tari kaine zaka nemeta amma ita bazata nemeka ba. Idan kuma ta nemeka wata bukata ce da ita da take son ka taimakamata.
Irin wadannan matan sunada wani can da suka ajiye shi a gefe da ahi5 suke so amma suke yaudaran wadanda suka gani da maiko. Don haka da zaran ka fahimci mace sai dai kaine zaka nemeta amma ita ko oho, kara gaba
3: Bata Tsayawa Da Kai:
Alama na gaba da zaka gane mace mai tara samari shine. Maganarku a waya yafi haduwar ku yawa. Haka kuma idan ma zaku hadu badai a kofar gidansu inda tasan za a iya ganinku ba. Ko wani wajen datasan da wani aka santa ba dakai ba.
Mace idan kai kadai take so duk inda aka kwana uku baka zo kofar gidan su ba zata hasala. Amma ita mai tara samari haka tafi so. Don haka da zaran ka fahimci wacce yanzu haka kake soyayya da ita kullum tana baka uzurin bata da lokacin ganin ka. Cikawa qandonka iska.
4: Bazata Yarda Kuyi Hoto Ba:
Duk yadda zakayi da mace mai tara samari bazata amince tayi hoto da kai ba muddin bata sonka. Idan ma zakuyi da wayanta za ayi yadda bayan ta rabu da kai zata goge. Kana cewa da wayarka za ayi hoton shirin zai wargaje.
Irin wadannan matan sun san samarin da suke so na shiga wayoyinsu su yi bincike, don haka ba zata taba yin kuskuren yin hoto da namijin da bashi take so ba.
Idan har Allah Yasa a yanzu haka ka gano itama wacce kake son haka take. Rabuda ita ko sallama kada kayi mata na bankwana.
5: Bazata Amince Ka Rike Wayanta Ba:
Duk yadda take maka kwarkwasa da fari bazata taba yarda ka taba mata waya ba muddin tasan ba kai kadai bane sarauyinta.
Irin wadannan matan cikin wayoyinsu hotuna ne jibge na ainihin samarinsu. Don haka baka wayar a hannunka yana iya zama karshen moranka datake yi.
Ita wayar hannu ga mata tamkar ransu ne, duk macen da zata baka wayanta ka rike kawai na mintuna 3 ba tare da kayi mata bincike ba tabbas wannan akwai yarda tsakaninku. Bare kuma macen da zata baka ka shiga duk inda kake so a cikin wayarta ka duba.
Don haka idan har matsayinka bai kai ta baka wayarta ka rike a hannunka ba, ka hakura kawai ba kai kadai take soyayya da shi ba. Akwai wani can a gefe na gasken.
Babu shakka mata suna dauka wani abun burgewa ne tara samari. Akwai wata al’ada da mata basu gano maza suna yiwa mace mai tara samari ba. A darasi na gaba zamu kawo shi domin matan da suke ganin kamar tara samari wayone, zasu gane gayye samarin ke hudawa suna kallonki da shi.