Yadda Shantaleliyar budurwa ta gayawa dan achaɓa ina sonka (bidiyo)
Wata budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a Soshiyal midiya bayan ta bayyana wa wani ɗan Acaba rassan ƙaunar da ya kafa a zuciyarta.
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin TikTok ya nuna yadda budurwar ta ja Ɗan Acaban da hira duk da yana jin kunya daga bisani ta zayyana masa cewa ya tafi da imaninta.legit na ruwaito
Mutumin wanda ya nuna kunya ya kawar da kansa ya yin da ta shafa masa kai, ta roke shi ya taimaka ya karɓe ta, ya gaya mata shi ma yana kaunarta
Yayin da ya saduda da bukatarta, Ɗan Acaban ya faɗa mata yana sonta daga nan kuma sai ta ba shi kyautar N20.
Ya sa hannu ya amsa cikin hamdala yayin da dirarriyar budurwar ta kama hanya ta bar wurin. Ga bidiyon Nan
Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu
Drey ya ce:
“Wata rana wani sai ya yi amfani dake wajen buga kalar wannan wasan.”
Korez 1 ya ce:
“Wai abinda nake gani ta ba shi N20 ce ko me? A dawo da bako ya sha kwai nawa ake hawa Babur ne.”
Lattojnr12 ya ce:
“Mutumin fa zai je ya gaya wa dukkan abokansa abinda ya faru amma ba zasu yarda ba, ina ganin sai ya yi mafarkin wannan.”
Onyeka XD yace:
“Abun tausayi an yi wasa da hankalin ɗan uwa.”
Kecho Man yace:
“Idan da namiji ne ya yi wa wata mace haka, da yanzu abun ya zama matsala.”