Labarai

Yadda na dinga danne albarkatun ƙirjina don kada mijin mamata yaga tudunsu ya lalata ni – cewar Mawaƙiya

Mawakiya Shania Twain ta bayyana cewa tana danne albarkatun kirjinta saboda gudun mijin mahaifiyarta, Jerry Twain ya lalata ta a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, dimokuraɗiya ta ruwaito.

Mawakiyar mai shekaru 50 ta ce Jerry Twain ya kasance yana cutar da ita yayin da take zama a gidansa kamar yadda The Sunday Times ta ruwaito.Yadda na dinga danne albarkatun ƙirjina don kada mijin mamata yaga tudunsu ya lalata ni - cewar  Mawaƙiya

Ta cigaba da cewa:

Ina boye kaina tare da danne albarkar kirjina. Ina sanya rigunan maman da suka yi min kadan.

“Wani lokacin har guda biyu nake sanyawa sannan in danne su yadda babu wani tudun jikin mace da zai bayyana a jikina. Hakan ya fi min sauki. Saboda ba za ka so zama mace a gidanmu ba.”

Twain ta fara wakoki tana da shekaru 8 da haihuwa inda ta dinga fama kafin ta amince cewa I ta mace ce saboda azabtarwa.

Ya bayyana yadda aka dinga cutar da ita a wani labarin rayuwarta da ta bayar a 2011, mai suna “Daga wannan Lokacin.

A cikin littafin, Twain ta bayyana cewa akwai lokutan da rikici ke hautsinewa tsakanin iyayenta har ta dinga tunanin mijin mamarta zai halaka mata uwa. Iyayenta sun rasu ne a lokacin tana da shekaru 22 da haihuwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button