Labarai

Yadda barin jikin Magidanci ya shanye ɓayan matarsa ta sanar da shi cewa ba shi bane asalin mahaifin yaransu 2

Wani dan Najeriya ya bayyana tashin hankalin da wani mutum ya shiga bayan matarsa ta sanar da shi cewa yaransu biyu ba nashi bane, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda @MeverickThamani ya bayyana a shafinsa ba Twitter, mutumin ya kai shekaru 50 da doriya kuma ‘yar uwarsa ce yanzu haka take kulawa da shi a asibiti sanna ita ce ta bayar da labarin abinda ya same shi.

Yadda barin jikin Magidanci ya shanye ɓayan matarsa ta sanar da shi cewa ba shi bane asalin mahaifin yaransu 2
Yadda barin jikin Magidanci ya shanye ɓayan matarsa ta sanar da shi cewa ba shi bane asalin mahaifin yaransu 2

Ta ce mutumin yana matukar kaunar matarsa wanda hakan yasa ya zabe ta a maimakon ‘yan uwansa. A bayan har yanke alaka yayi da ‘yan uwansa sai daga baya ya kama ta tana lalata da wani namiji.

Wannan ne ya janyo rikici ya barke tsakaninsu har ta kai ga sanar da shi cewa yaransu ba nashi bane. Ana tsaka da rikicin ne ta bayyana masa wannan mummunan labarin wanda yasa ya fadi kasa bayan ya yanke jiki, hakan yayi sanadiyyar shanyewar barin jikinsa.

Bayan ganin halin da yake ne matar ta tsere ta kwashe kudi daga asusun bankinsa tare da guduwa da yaran. Yanzu haka yana zama ne karkashin ‘yan uwansa inda suke kulawa da shi kamar yadda mutumin ya bayyana a Twitter.

Wani labari Ban san ina da ciki ba, inji budurwar da ta haihu a jirgin sama

Wata budurwa wacce bata san tana da ciki ba ta haihu jirgi na sararin samaniya. Matar mai suna Tamara ta kwashi hanya ne zata wuce Ecuador daga Madrid, Spain a jirgin KLM Royal Dutch.

An samu bayani kan yadda Tamara kwatsam ta hau jirgi wanda ana gab da isa Netherlands ta fara jin ciwon ciki. Sakamakon jin ciwo, Tamara ta nufi bandaki inda ta nemi yin bayan gida kawai sai haihuwa ta yi.

Kamar yadda Daily Star ta ruwaito, Tamara ta haihu ne bayan yunkurin nakuda biyu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button