Labarai

Wasu magoya bayan Faransa sun nemi a sake wasan su da Argentina



Kwanaki bayan kammala wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta 2022 da aka yi a Qatar, wasu magoya bayan tawagar Faransa sun yi kira da a sake buga wasan da Argentina.

Ku tuna cewa kungiyar kwallon kafa ta Argentina ta lallasa Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi kunnen doki tsakanin bangarorin biyu bayan karin lokaci.fmdala na ruwaito

Wasu magoya bayan Faransa sun nemi a sake wasan su da Argentina
Wasu magoya bayan Faransa sun nemi a sake wasan su da Argentina

Faransa da Argentina a lokacin wasan sun zura kwallaye uku kowannensu, sakamakon kwazon da ‘yan wasan Paris Saint Germain, Kylian Mbappe da Lionel Messi suka yi.

Argentina ta doke Faransa da ci 4-2 a bugun fenariti bayan da aka tashi 3-3 bayan karin lokaci.

Sai dai an samu wasu lokuta masu tada hankali yayin wasan inda magoya bayan Faransa suka nuna rashin jin dadinsu kan wasu hukunce-hukuncen alkalan wasa.

Ci gaban da aka samu ya sa wasu daga cikinsu sun gabatar da takardar neman a sake buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta FIFA.

Kokarin ya na samun karbuwa sosai yayin da kusan mutane 200,000 suka sanya hannu.

‘France 4Ever’ ce ta kaddamar da koken na a sake buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 tsakanin Argentina da Faransa.









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button